Ekiti: Tarihin Gwamnonin farar hula daga 1999 zuwa yanzu

Tun bayan dawowar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, Jihar Ekiti ta kasance ɗaya daga cikin jihohin kasar da ake bibiyar siyasar ta a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Otunba Niyi Adebayo na jam’iyyar AD ne ya zama gwamna na farko da aka zaɓa a jihar, inda ya yi mulki daga shekarar 1999 zuwa 2003.

A shekarar 2003, Ayodele Fayose na PDP ya lashe zaɓe kuma ya yi mulki har zuwa shekarar 2006, lokacin da rikicin siyasa ya kai ga tsige shi daga mukaminsa, tare da ayyana dokar ta-baci a jihar.

Segun Oni na PDP, ya zama gwamna a shekarar 2007, amma shari’o’in zaɓe ne suka biyo baya har zuwa shekarar 2010 lokacin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ayyana Dr. Kayode Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Dr. Kayode Fayemi na ACN ya yi mulki daga shekarar 2010 zuwa 2014, kafin Ayodele Fayose ya sake dawowa kan mulki bayan nasarar da ya samu a zaɓen 2014.

Fayose ya yi wa’adinsa na biyu daga shekarar 2014 zuwa 2018, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin gwamnonin da suka yi wa’adi biyu, wanda ba a jere ba.

A shekarar 2018, Kayode Fayemi ya sake dawowa mulki karkashin jam’iyyar APC, inda ya yi wa’adinsa na biyu har zuwa shekarar 2022.

Bayan zaɓen shekarar 2022, Biodun Abayomi Oyebanji na APC ya zama gwamnan jihar, kuma shi ne ke jagoranta a halin yanzu.

Masana siyasa na ganin cewa tarihin siyasar Ekiti ya nuna sauyin mulki tsakanin PDP da APC, tare da muhimmiyar rawar da kotuna suka taka wajen sauya shugabanci a wasu lokuta.

Haka kuma, Ayodele Fayose da Kayode Fayemi sun kasance gwamnoni biyu kacal da suka yi wa’adi biyu ba a jere ba, abin da ke nuna irin gasa da fafatawar siyasa da ake samu a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *