Gwamnan jihae Ekiti Biodun Oyebanji ya sha lawashin ƙara ƙwazo don cimma tattalin arziƙi mai ɗorewa da rage fatara da kuma faɗaɗa  samar da damammaki ga mazauna jihar, biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamna a jihar.

Oyebanji ya samu jimlar ƙuri’u 319,224, inda ya kada abokin hamayyarsa mafi kusa a zaɓen da aka yi a faɗin ƙanana hukumomi 16 dake faɗin jihar.

Da yake yi wa taron magoya bayansa jawabi jim kaɗan baya nasarar tasa a ranar Lahadi, gwamnan ya bayyana sakamakon zaɓen a matsayin wata sabuwar dama don ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ta samu nasarar aiwatar wa.

Ya kuma bayyana cewa yanzu zai fara baje kolin ayyukan alheri, yana mai ƙarawa da cewa nasarar zaɓen wani kaimi ne gare shi da gwamnatinsa don su yi aiki wurjanjan wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati da aka tsara don samar da nagartatcciyar rayuwa ga mazauna jihar.

Gwamna Oyebanji ya ƙara da cewa: ‘za mu sake sadaukar da kawunanmu fiye da da wajen aiwatar da manufofi masu kyawu. Za mu hanzarta kamala ayyuka daban-daban da a yanzu haka ake kan gudanar da su. Za mu yi aiki tuƙuru kuma cikin basira fiye da da don bauta muku’.

Ya jaddada cewa babban burin gwamnatinsa shi ne kawar da fatara da kuma rage rashin adalci da daidaito, yana mai lura da cewa ci gaba zai zamo mai tasiri ne kaɗai idan ya haifar da kyautata yanayin rayuwar talaka.

‘Ba za mu huta ba har sai mun tabbar fatara da rashin daidaito sun zama tarihi a jihramu’, in ji gwamana Oyebanji ’

Sai gwaman ya sadaukar da nasarar zaen da ya samu ga ɗaukacin al’umar jihar Ekiti, yana mai bayyana sakamakon da cewa ‘yar manuniya ce ga irin ƙwarin gwiwar da al’umar jihar ke shi ga yadda gwamanatisa ke gudanar da ayyukanta.

Ya yi alƙawarin cewa ba zai taɓa cin amanar da aka ɗora masa ba; ya kuma tabbabatar wa mazauna jihar cewa gwmnati za ta mai da hankali wajen samar da ayyuka masau tasirin gaske, waɗan da suka haɗa da ayyukan more raywa da ilimi da kiwon lafiya da kuma samar wa da mata ayyukan yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *