Ƙungiyar Democratic Youth Assembly of Nigeria ta sake jaddada goyon bayanta ga Rundunar Sojojin Najeriya (Armed Forces of Nigeria), tare da yin alƙawarin yin aiki tare da Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (Defence Headquarters) domin inganta zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da wayar da kan jama’a kan batutuwan tsaro a faɗin ƙasar nan.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai, Harkokin Watsa Labarai da Sadarwa ta Musamman na ƙungiyar, Kwamared Sadik S.K. Zango, ya sanya wa hannu bayan wata ziyarar girmamawa da shugabanni da mambobin ƙungiyar suka kai Hedikwatar Tsaro da ke Abuja.
A cewar sanarwar, Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar O.O. Oluyede, wanda Rear Admiral S.A. Lawal, Babban Jami’in Hulɗar Sojoji da Fararen Hula ya wakilta, ya gode wa ƙungiyar bisa ziyarar tare da yabawa matasan Najeriya kan ƙara nuna sha’awa ga ci gaban ƙasa da harkokin tsaro. Ya bayyana cewa haɗin gwiwa da ƙungiyoyin matasa na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
- Gwamnatin Tarayya za ta baiwa jihohi Kuɗaɗe kan barazanar Cututtuka
- Abdul-aziz Yari ya nesanta kansa da ɗaukar nauyin zanga-zanga kan Gwamnati
- Wane ne Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Ekiti?
Sai dai ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ba hukumomin tsaro cikakken goyon baya da jagoranci domin shawo kan matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.
Haka kuma ya ce Rundunar Sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da na leƙen asiri na ci gaba da gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na ƙasar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, dawo da zaman lafiya da kuma kare cikakken ikon ƙasar.
Janar ɗin ya kuma yi kira ga matasan Najeriya da su guji tashin hankali, tsattsauran ra’ayi, yaɗa ƙarya da duk wani nau’in laifi, sannan su rungumi tattaunawa, zaman lafiya da haɗin kai a matsayin hanyoyin ci gaban ƙasa. Ya kuma buƙace su da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai, su yi amfani da kafafen sada zumunta yadda ya dace, tare da zama jakadun zaman lafiya a cikin al’ummominsu.
A nasa jawabin, Mai Kula da Ƙungiyar a Matakin Ƙasa, Ambasada Bashir Nasiru Garki, ya yaba wa Rundunar Sojojin Najeriya bisa sadaukarwa da ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar. Ya ce galibin nasarorin da sojoji ke samu kan ɓace a idon jama’a saboda yaɗa bayanan ƙarya da farfaganda, duk da irin ci gaban da ake samu a wuraren gudanar da ayyukan tsaro.
Garki ya kuma nemi a samar da haɗin gwiwa a hukumance tsakanin ƙungiyar da Hedikwatar Tsaro domin inganta zaman lafiya, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma wayar da kan jama’a game da batutuwan tsaro. Haka nan ya yi alƙawarin cewa matasan Najeriya za su taimaka wajen yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya da ake yi kan Rundunar Sojojin Najeriya.
A ƙarshe, ƙungiyar ta bayyana cikakken amincewarta da jagorancin Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, tare da yabawa salon shugabancinsa na kasancewa a gaba wajen jagorantar ayyuka, yawan kai ziyara wuraren aiki, kula da jin daɗin sojoji da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da tsaron ƙasa.