An ayyana dan takarar jamiyyar APC a zaɓen cike gurbi a Mazabar ɗan Majalisar Dattawa ta Nasarawa Ta Arewa, da aka gudanar ranar Asabar, Envu-Alanza, a matsayin wanda ya samu nasara.

Mai bayyana sakamakon zabe Farfesa Aminu Ali ya sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen a cibiyar tattara sakamakon zaɓen dake Kwalejin Ilimi dake Akwanga, bayan tattara sakamakon daga ƙananan Hukumomin Akwanga da Nasarawa Eggon da kuma Wamba.

Kamar yadda sakamakon ya nuna, Envu-Alanza ya samu ƙuri’u 45,362, abin da ya ba shi nasara kan abokin karawarsa , tsohon ministan yaɗa labarai, Labaran Maku na jam’iyyar Labour Party, wanda ya samu jumillar ƙuri’u 12,931.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *