Manchester City ta amince da yarjejeniya da Nottingham Forest don siyen Elliot Anderson.
An fahimci cewa kuɗin sayen dan wasan zai kai fam miliyan 116, wanda zai karya tarihin sayayyar ’yan wasa na City, kuma zai sa Anderson ya zama ɗan wasan Biritaniya mafi tsada a tarihin ƙwallon ƙafa.
Dan wasan mai shekaru 23 yana da kwantiragi da kungiyar ɗin na Midlands har zuwa 2029 kuma shi ne babban burin Man City a tsakiya wannan bazara.
-
Scotland 0-3 Brazil: Vinicius ya kafa tarihi
-
Gusau ya yi alkawarin mayar da horar da masu horarwa zuwa matakin jihohi
Anderson ya fito a matsayin ɗaya daga cikin ’yan wasan tsakiya mafi kyau a gasar firimiya a kakar da ta gabata.
Yana cikin jerin manyan ’yan wasan tsakiya da tauraruwar su ke haskawa a wannan bazara, ciki har da Sandro Tonali na Newcastle, Adam Wharton na Crystal Palace da Carlos Baleba na Brighton.
A yanzu haka Anderson yana Amurka tare da tawagar Ingila a Kofin Duniya, inda ya fara wasanninsu biyu na rukuni har zuwa yanzu.
