Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (DIG) mai kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya, Isyaku Mohammed, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ba za ta ɗauki ko ta shigar da tsofaffin ‘yan ta’adda cikin aikinta ba.
Mohammed ya bayyana haka a Ilori, yayin wata ganawa da jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai,, ƙungiyoyin sufuri da sauran masu ruwa da tsaki.
Sai dai ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da kada su ba da shawarwari ko rubuta takardun goyon baya ga masu aikata laifuka da suka san tubabbu ne, domin shiga hukumomin tsaro.
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon titin mahaɗar hanyar Jahi zuwa Gwarimpa a Abuja
- ’Yan sanda sun ceto mutum 9 daga hannun ‘yan bindiga a Kaduna, jami’ai biyu sun rasa rayukansu
- Ƙudirin kafa ’yan sandan jihohi na ƙara samun goyon baya a Nijeriya
Maimakon haka, su riƙa tona musu asiri domin kada su samu damar shiga aikin tsaron.
Ya ƙara da cewa, “Na taba yin aiki a Arewa maso Gabas, Sojoji bisa hikima suka karɓi wasu tsofaffin ‘yan Boko Haram suka sake tarbiyyantar da su, sannan suka mayar da su cikin al’umma.”
DIG Isyaku ya ce wannan mataki na gwamnatin tarayya ne, kuma rundunar ‘yan sanda ba za ta iya canza shi ba.