Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta samu nasarar ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, yayin da jami’anta biyu suka rasa rayukansu a wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai musu bayan kammala aikin ceton.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar ranar Alhamis, ya ce rundunar ta samu sahihan bayanan sirri da misalin ƙarfe 12:45 na rana a ranar 24 ga Yunin 2026 cewa wasu ’yan bindiga kusan 15 ɗauke da muggan makamai sun yi garkuwa da wasu manoma a yankin Unguwan Sa’idu da ke kusa da garin Birnin Gwari.

Sanarwar ta ce nan take kwamandan yankin Birnin Gwari da shugaban ofishin ’yan sanda na yankin suka haɗa tawagar jami’an sintiri tare da jami’an rundunar PMF da na KADVIS domin gudanar da aikin ceto.

A cewar rundunar, da isarsu wurin sun yi arangama da ’yan bindigar, lamarin da ya sa maharan suka fara tserewa cikin daji a kan babura bayan sun gamu da turjiya daga jami’an tsaro.

Rundunar ta ce jami’anta sun bi sawun maharan, wanda hakan ya tilasta musu yin watsi da mutanen da suka sace tare da tserewa.

Mutane tara da aka ceto sun haɗa da Hudu Rabiu mai shekara 31 da Yusuf Sagir mai shekara 20 da Sagir Rabiu mai shekara 17 da Muhammad Kabir mai shekara 23 da Kabir Lawal mai shekara 20 da Idris Abubakar mai shekara 17 da Mustapha Zayyanu mai shekara 18 da Kabiru Rabiu mai shekara 18 sai kuma Usman Lawal mai shekara 18.

Sanarwar ta ce an same su ɗaure da igiyoyi, amma an ceto su ba tare da sun ji rauni ba, sannan aka mayar da su ga iyalansu.

Sai dai rundunar ta bayyana cewa yayin da jami’an ke dawowa daga aikin, wasu da ake zargin ’yan bindiga sun yi musu kwanton ɓauna a kan hanya.

A sakamakon harin, jami’an ’yan sanda biyu sun samu raunukan harbin bindiga kuma daga bisani suka rasu yayin da suke bakin aiki.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya jajanta wa iyalan jami’an da suka rasu, abokansu da kuma abokan aikinsu.

Ya bayyana sadaukarwar da suka yi a matsayin wata alama ta jarumtaka, jajircewa da kuma kishin aikin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike da kuma wasu ayyukan tsaro domin gano waɗanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *