Wasu mahara da ake zargin mambobin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne sun kai hari Makarantar Sakandaren Gwamnati ta rana da ke Lassa, a Ƙaramar Hukumar Askira/Uba ta jihar Borno, inda suka yi garkuwa da adadin ɗaliban da ba a tantance ba da ke rubuta jarabawar NECO.
Rahotanni sun ce maharan sun mamaye makarantar ne da misalin ƙarfe tara na safe, inda suka riƙa harbe-harbe a sama, lamarin da ya jefa ɗalibai, malamai da mazauna yankin cikin firgici, kafin su tafi da wasu daga cikin masu rubuta jarabawar zuwa cikin daji.
An kuma ce wani malami ya rasa ransa a harin, yayin da wani ya samu raunuka.
-
’Yan sanda na bincike kan mutuwar Malamar makaranta
-
Trump: Amurka ta kawo ƙarshen kisan kirista a Najeriya
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya ce har yanzu akwai wasu ɗalibai da ba a san inda suke ba.
Ya ce maharan da ake zargin ‘yan Boko Haram da ISWAP ne sun kai harin makarantar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, inda suka yi ta harbe-harbe a sama tare da yin garkuwa da wasu ɗalibai, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu da suka ɓace.
Sai dai ya ce rundunar ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa akwai waɗanda suka mutu a cikin waɗanda abin ya shafa ba.
Hakan na zuwa ne, daidai lokacin da rahoton Amnesty ke cewa ansa ce yara 81 daga makarantu a jihohin Borno da Oyo a ranar 15 ga Mayun 2026 na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da su, bayan shafe kwanaki 45 ba tare da an kuɓutar da su ba.
Sanarwar ta ce ba a san irin halin da yaran ke ciki ba, yayin da iyayensu ke ci gaba da rayuwa cikin damuwa.
Ta kuma jaddada cewa hare-haren da ake kai wa makarantu na saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, tare da kira ga hukumomin Nijeriya su ƙara kare makarantu da rayukan yara, su gudanar da cikakken bincike kan irin waɗannan hare-hare, tare da tabbatar da an gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata su a gaban kotu bisa adalci.