Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yabawa Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya bisa rawar da take takawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kare muradan ƙasa, yana mai cewa rundunar ta zama abin alfahari ba kawai ga Najeriya ba, har ma ga nahiyar Afirka da duniya baki ɗaya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin bikin rufe Ranar tunawa da Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya (NADCEL) 2026 da aka gudanar a Filin Wasanni na Liberation da ke Port Harcourt, Jihar Rivers.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya wakilci Shugaban Ƙasar a wajen bikin.

Shugaba Tinubu ya ce Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta ci gaba da nuna jajircewa da ƙwarewa da nagarta tun daga shiga manyan yaƙe-yaƙe na duniya zuwa ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) da kuma ayyukan tsaro a nahiyar Afirka.

Ya ce irin gudummawar da rundunar ke bayarwa ta taimaka wajen kare ikon Najeriya tare da ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Afirka.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa rundunar ta hanyar zamanantar da kayan aikinta da inganta walwalar jami’ai da sojoji da kuma samar da sabbin fasahohi domin tunkarar sabbin barazanar tsaro.

Bikin na NADCEL 2026 ya ƙunshi faretin sojoji da baje kolin dabarun yaƙi da kayan aikin soja tare da karrama jami’an da suka yi fice da lambobin yabo na Hafsan Sojin Ƙasa.

Haka kuma an gudanar da baje kolin bincike da ci gaban fasaha, inda rundunar ta nuna irin nasarorin da ta samu wajen ƙera kayayyakin tsaro da bunƙasa fasahar cikin gida domin tunkarar ƙalubalen tsaro na yanzu da na gaba

Sai dai Najeriya ta sha fama da rikice-rikice tun daga  shekara ta 2009 da Boko Haram ta ɓulla da kuma na ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, kazalika akwai rikicin ƙungiyar IPOB da yaƙi ci yaki cinyewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *