Rundunar ‘Yan Sandan Birnin Tarayya Abuja ta kama mutane 560 da take zargi da hannu a laifuka daban-daban, bayan jerin sumame da ta kai wuraren da ake zargin masu aikata laifuka ke buya a sassan Abuja.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Ahmed Mohammed Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
Ya ce an gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da al’umma ke yi da jami’an tsaro, domin daƙile ayyukan masu aikata laifuka a Babban Birnin Tarayyar.
Sanusi ya ce jami’an rundunar sun kama waɗanda ake zargi tare da ƙwato bindigogi ƙirar gida guda biyu, ciki har da wadda aka ƙera mai kama da AK-47, harsasai uku masu rai na bindigar milimita tara, da miyagun ƙwayoyi tare da wasu kayayyakin da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifuka.
Ya kuma bayyana cewa rundunar ta tarwatsa wata ƙungiya mai mutum shida da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma aikata satar fasinjoji ta hanyar da aka fi sani da “One Chance.”
Bincike ya nuna cewa ƙungiyar ta yi garkuwa da wata mata a yankin Maitama, inda ta karɓi kuɗin fansa har naira miliyan takwas da dubu ɗari biyu da hamsin daga iyalanta.
Kwamishinan ya ce bincike ya nuna cewa ƙungiyar ta shafe kusan shekaru biyu tana gudanar da ayyukanta a kan titin Kubwa Expressway da Maitama Federal Housing da wasu sassan Abuja, inda ake zarginta da karɓar kusan naira miliyan goma sha biyu da dubu ɗari takwas daga mata aƙalla biyar.
Sanusi ya ce jami’an rundunar sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma safarar harsasai da miyagun ƙwayoyi ga ‘yan bindiga, yayin wani samame da aka gudanar a yankunan Kwali da Abaji da Kuje.
Kwamishinan ya jaddada cewa rundunar tasa za ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka har sai an tabbatar da tsaro da zaman lafiya a babban birnin tarayya Abuja.