Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon tsari na lambobin shaida ga ɗaliban ƙasar nan mai suna Learner Identification Number a turance.

Ministan Ilimi na Najeriya Maruf Tunji Alausa ya bayyana yunkurin a matsayin wani babban sauyi mai cike da tarihi, da ya dace da manufofin Gwamnatin.

Ministan ya ce a matakin farko an riga an bai wa dalibai sama da miliyan 1.9 da za su zauna jarrabawar kammala sakandire ta shekarar 2026 lambar shaidar ta LIN.

Tsarin zai bai wa hukumomi damar taskance bayanan ɗalibi domin bibiyar nasarorin da yake kai tun daga matakin farko zuwa karshen karatunsa.

Ministan ya ce za a faɗaɗa tsarin zuwa dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *