Tsohon mai taimaka wa shugaban ƙasa, Kingsley Kuku, ya bayyana cewa babbar matsalar tsaron Najeriya ba ta’addanci ba ce, ba fashi da makami ko garkuwa da mutane ba, sai dai raguwar amincewar jama’a ga ikon gwamnati na kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Kuku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin da yake gabatar da laccar bankwana mai taken: “Ƙasar Najeriya Cikin Ƙunci: Tsarin Mulki da Muhimmancin Sabunta Ƙasa,”da aka gudanar a wajen bikin bankwana na ɗaliban da suka kammala karatun digiri na shekarar 2026 a Kwalejin Shari’a ta Oba Erediauwa, Jami’ar Igbinedion da ke Okada.
Ya bayyana cewa taɓarɓarewar tsaro a ƙasa na nuna wata babbar matsala ta tsarin mulki, inda ‘yan Najeriya da dama suka gaza amincewa da hukumomin gwamnati da ke da alhakin kare rayuka da dukiyoyin su.
- Ƙungiyar Lauyoyi Ta Najeriya ta zaɓi Badejo-Okusanya a matsayin shugaba
- A na iya kawo karshen matsalar yaran da basa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya – Prof Abbas
- Dakarun Operation HAƊIN KAI sun daƙile yunƙurin sace ɗalibai a FGGC Monguno
A cewarsa, babbar barazanar ita ce ƙaruwar rashin amincewa tsakanin jama’a da gwamnati.
Ya yi gargaɗin cewa dimokuraɗiyyar tsarin mulki na shiga haɗari idan mutane ba su ƙara yarda cewa hukumomin doka za su iya kare su ba.
Tsohon shugaban Shirin Afuwa na Shugaban Ƙasa (Presidential Amnesty Programme) ya ce yawaitar dogaro da ƙungiyoyin sa-kai da jami’an tsaro na yankuna maimakon hukumomin tsaron da kundin tsarin mulki ya tanada, alama ce da ke nuna girman matsalar.
Kuku ya ce hanyar magance matsalolin tsaro a Najeriya ita ce sake gina amincewar jama’a ta hanyar ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, tabbatar da shugabanci nagari, samun ‘yancin cin gashin kai ga ɓangaren shari’a da kuma bin doka da kundin tsarin mulki.