Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito a baya cewa Malama Badejo-Okusanya, wadda ita ce kadai mace a cikin ‘yan takara uku da suka tsaya takarar shugabancin Ƙasar, ta samu ƙuri’u 12,317 inda ta lashe zaɓen da aka gudanar ta hanyar na’ura mai ƙwaƙwalwa na tsawon sa’o’i 24, tun daga ƙarfe 7:35 na safe a ranar Asabar zuwa ƙkarfe 7:34 na safe a ranar Lahadi.
- Mun kafa tarihin da ba za a taɓa gogewa ba – Lionel Messi
- A na iya kawo karshen matsalar yaran da basa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya – Prof Abbas
- Za mu kama Netanyahu idan ya halarci Taron Majalisar Ɗinkin Duniya – Mamdani
Wannan babbr lauyar ta doke abokan takararta maza guda biyu, inda ta samu kashi 47.18 cikin ɗari na ƙuri’u 26,106 da aka kada a zaɓen shugabancin ƙasar, bisa ga sakamakon ƙarshe da ke kan shafin nuna sakamakon zabe kai-tsaye (Live Election Results dashboard) wanda Kwamitin Zabe na NBA (ECNBA) ke kula da shi.
Lateef Omoyemi Akangbe, SAN, ya samu ƙuri’u 7,934 (kashi 30.39 cikin ɗari) inda ya zo na biyu, yayin da Olumuyiwa Akinboro, shi ma wani SAN, ya samu ƙuri’u 5,855 (kashi 22.43 cikin ɗari) inda ya zo na uku.
Zaɓen na dukkan muƙaman ƙasa guda 13 na ƙungiyar ya sami ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a: masu jefa ƙuri’a 26,184 ne kawai suka shiga zaɓen, wanda hakan ke wakiltar kashi 31.86 cikin ɗari kacal na jimillar masu zaɓe 82,172 da aka yi wa rajista.