Sojojin rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA (JTF NW OPFY), sun ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su bayan da suka dakile harin ’yan ta’adda a kauyen Magami da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi 26 ga Yuli, 2026, bayan da sojojin Runduna ta 2 suka samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan ta’adda dauke da babura kusan 40 sun mamaye kauyen.
- Abacha: A daina yaɗa ƙarya kan matattu, Al-Mustapha ga tsohon jami’in DSS
- Sojoji sun fara aikin ceto Shugaban ƙaramar Hukumar Bunguɗu
- Gwamna Sule ya bai wa Nasarawa Amazons da sauran ƙungiyoyin wasanni kyautar kuɗi da mota
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun yi awon gaba da wasu mazauna yankin domin kai su cikin daji, yayin da wani bangare daga cikinsu ya tsaya a wajen kauyen tare da baburan da suka yi amfani da su.
Sojojin sun samu nasarar ceto dukkan mutane 48 da aka sace, yayin da aka tabbatar da mutuwar wani farar hula a yayin harin.
Har ila yau, an ruwairo cewa wasu mutane biyu kuma sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an kai su Babban Asibitin Kauran Namoda domin samun kulawar likta.
Bayan aikin ceton, sojojin sun kara karfafa sintiri a yankin, domin tabbatar da tsaro da hana sake aukuwar irin wannan hari.