Gwamnatin Jamus ta fitar da ƙa’idojin zama da dole baƙi su cika kafin su nemi samun takardar zama ɗan ƙasar Jamus.
A cewar gwamnatin, lokacin da mutum ya yi yana zaune a ƙasar ƙarƙashin dakatar da korar sa na wucin gadi (Duldung) ba za a ƙirga shi cikin shekarun zama na doka da ake buƙata ba.
Haka kuma, masu neman mafaka (asylum seekers) suna da wasu takamaiman sharudda da ke tantance ko lokacin da suka yi a Jamus za a hada ahi cikin ƙidaya wajen cancantar neman zama ‘yan ƙasar.
Jamus ta tabbatar da cewa duk wani baƙon da ke son neman zama ɗan ƙasar dole ne ya kasance ya yi aƙalla shekaru biyar yana zaune a ƙasar bisa doka kafin ya cancanci yin wannan buƙata.
- ƙara tsananta matakan soji kan Iran
- Lauyoyi sun buƙaci a saki tsohon Shugaban Nijar bayan cika shekaru uku da juyin mulki
- Guterres ya yi kira ga Duniya ta taimaka wa Siriya bayan y
A cewar gwamnatin Jamus, waɗannan shekaru biyar dole ne su kasance ba tare da yankewa ba, wato mai neman takardar ɗan ƙasa ya kasance yana zaune a Jamus ba tare da katsewa ba, kuma har yanzu yana zaune a ƙasar lokacin da ya gabatar da buƙatarsa.
Gajerun tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje domin hutu ba sa karya wannan ci gaba na zama.
Sai dai, duk lokacin da mutum ya yi a Jamus ƙarƙashin izinin dakatar da kora na wucin gadi (Duldung) ba za a ƙirga shi cikin shekarun biyar ba.
Ga masu neman mafaka kuwa, lokacin da suka yi suna jiran a yanke hukunci kan buƙatarsu zai ƙidayu ne kawai idan daga ƙarshe aka amince da su a matsayin: