Lauyoyin da ke kare tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, sun yi kira da a gaggauta sakin shi, shekaru uku bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa tare da tsare shi.
An zaɓi Bazoum, mai shekaru 66, a matsayin shugaban ƙasa a shekarar 2021. Sai dai tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023, shi da matarsa, Hadiza Bazoum, ke tsare a wani ɓangare na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Niamey
Ƙungiyar lauyoyin ƙasa da ƙasa da ke kare Ba.zoum ta bayyana cewa ana tsare da shi ba bisa ƙa’ida ba.
- ‘Yan takara 6 na neman maye gurbin Guterres a Majalisar Ɗinkin Duniya
- Gobarar daji na ci gaba da tashi a Turai, mutum 200,000 sun bar muhallansu
- Shugaban Ƙasar Bangladesh ya yi murabus sakamakon rashin lafiya
Lauyan kare haƙƙin bil’adama ɗan Amurka, Reed Brody, tare da wasu lauyoyi daga ƙasashen Yammacin Afirka, sun ce ba a taɓa gurfanar da Bazoum da matarsa a gaban kotu ba, kuma ba a sanar da su cewa akwai wata shari’a da ake yi a kansu ba.
Sun kuma ce tun bayan tsare su, ba a ba ma’auratan damar mu’amala da jama’a yadda ya kamata ba, kuma cikin shekaru uku da suka gabata ba su samu ziyara daga ‘yan uwansu ba.
Bayan wasu watanni da juyin mulkin, gwamnatin sojin da Janar Abdourahamane Tiani ke jagoranta ta bayyana aniyarta ta gurfanar da Bazoum a gaban kotu
Gwamnatin ta zarge shi da cin amanar ƙasa da kuma kitsa makirci da ke barazana ga tsaro da ikon ƙasa, amma har zuwa yanzu ba a buɗe wata shari’a a hukumance a kansa ba.
Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da masana na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da kuma shugabannin ƙasashe da dama sun yi kira da a saki Bazoum.
Duk da cewa wa’adin mulkinsa ya ƙare a watan Afrilun wannan shekara, Bazoum ya ci gaba da ƙin yin murabus daga muƙaminsa.
Tun bayan karɓar mulki, gwamnatin sojin Nijar ta tsaurara matakai kan masu adawa da ita, inda ta tsare ‘yan jarida, masu rajin kare haƙƙin bil’adama da kuma wasu fitattun mambobin ƙungiyoyin fararen hula.