Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), António Guterres, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙara tallafa wa al’ummar Siriya yayin da ƙasar ke ƙoƙarin farfaɗowa daga mummunan yaƙin basasa da ya shafe fiye da shekara goma yana gudana.
Guterres ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata muhimmiyar ziyara da ya kai birnin Damascus, wadda ita ce ta farko da Babban Sakataren MDD ya kai babban birnin Siriya tun shekarar 2009.
Yaƙin basasar Siriya ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyin jama’a da muhallansu, kafin ya kawo ƙarshe a shekarar 2024 bayan ‘yan tawaye sun hambarar da tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad.
- Shugaban Ƙasar Bangladesh ya yi murabus sakamakon rashin lafiya
- Trump ya gargaɗi Chana ko Rasha da kar su ba wa Iran makamai
- ‘Yan takara 6 na neman maye gurbin Guterres a Majalisar Ɗinkin Duniya
Jagoran ‘yan tawayen, Ahmed al-Sharaa, wanda aka naɗa shugaban riƙon ƙwarya a watan Janairun 2025, na jagorantar ƙoƙarin sake gina ƙasar da kuma rusa ƙungiyoyin makamai masu zaman kansu.
Bayan ganawarsa da Ahmed al-Sharaa jim kaɗan bayan isarsa Damascus, Guterres ya ce Siriya na cikin wani muhimmin mataki na komawa kan turbar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Rahotanni sun nuna cewa barnar da yaƙin ya haifar za ta buƙaci biliyoyin daloli domin sake gina ƙasar.
Ko da yake Amurka da ƙasashen Turai sun sassauta yawancin takunkuman da suka ƙaƙaba wa gwamnatin Bashar al-Assad, har yanzu jama’a ba su fara ganin gagarumin sauyi a rayuwarsu ba.
Haka kuma, rage tallafin ƙasashen waje ya ƙara jefa al’ummar Siriya cikin mawuyacin hali. A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, kusan kashi 90 cikin 100 na al’ummar ƙasar na rayuwa cikin talauci.
A bara, Bankin Duniya ya fitar da wani rahoto da ya ƙiyasta cewa sake gina Siriya bayan fiye da shekaru goma na yaƙin basasa zai ci kusan dala biliyan 216.