Ministan Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Muhammad Idri Malagi, ya bayyana gamsuwarsa da sabon ɗakin shirye-shiryen talabijin na zamani da aka kammala ginawa a hedikwatar Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da ke Abuja.

Ministan ya ce aikin na daga cikin manufofin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na zamanantar da tsarin watsa labarai da kuma inganta ayyukan kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnati.

Muhammad Idris ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin da ya kai ziyara domin duba sabbin wuraren da aka inganta a hedikwatar NTA da kuma Cibiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (National Press Centre) da ke Radio House, Abuja.

Ya ce sabon ɗakin shirye-shiryen NTA yana daga cikin mafi ingancin wuraren watsa shirye-shirye a Najeriya da Afirka, yana mai cewa hakan ya nuna ci gaban da ake samu wajen sauya fasalin harkar watsa labarai a ƙasar.

Ya bayyana cewa shirin zamanantar da kafafen watsa labarai ya shafi NTA, Hukumar Rediyon Tarayya ta Najeriya (FRCN), Muryar Najeriya (VON) da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Ministan ya yaba wa shugabanci da ma’aikatan NTA bisa rawar da suke takawa wajen inganta ayyukan hukumar, yana mai cewa sauye-sauyen sun haɗa da inganta shirye-shirye, ƙwarewar ma’aikata, kirkire-kirkire da amfani da fasahar zamani.

Ya ƙara da cewa sayen sabbin kayan aikin watsa shirye-shirye da ake shirin rabawa tashoshin NTA a faɗin ƙasar zai taimaka wajen samar da ingantaccen aikin watsa labarai ga jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *