Tawagar Harambee Starlets ta ‘yan matan kasar Kenya za ta fafata da Teranga Lionesses ta ƙasar Senegal a wasan rukuni na A na Gasar cin Kofin Mata na nahiyar Afirka, WAFCON, 2026 ranar Alhamis a filin wasa na Olympic da ke Rabat, Moroko.
Kowannen su na neman nasara a wannan fafatawa domin cika burin su na zuwa mataki na gaba a gasar.
Duka ƙasashen biyu sun sha kaye a wasan su na farko na rukunin A, yayin da rashin nasara ga kowace tawaga ka iya kawo ƙarshen burin su na ci gaba da zama a gasar.
-
Neymar ya tabbatar da yin ritaya daga Brazil
-
WAFU B U20: Fying Eagles za ta kara da Sparrow Hawks
-
WAFCON: Yadda Scorchers suka gasa wa Super Falcons aya a hannu
Kenya ce ta fara shan kashi a hannun mai masaukin baƙi wato Moroko da ci 4-0, kafin daga baya Algeria ta lallasa Senegal da ci 2-0.
Wannan ne karo na farko da Kenya za ta fafata da Senegal a Gasar WAFCON, wasan da ake kyautata zaton zai dauki zafi.
Amma ƙasashen biyu sun kara a wasan sa da zumunci na ƙasa da ƙasa da suka buga a ranar 18 ga watan Nuwambar 2025, inda Senegal ta yiwa Kenya dukan shinkafar hashimu da ci 8-0.
A wani labarin na daban, ƙasashen Ghana da Kamaru sun fara Gasar WAFCON ta 2026 da ƙafar dama, inda suka yi nasarar doke abokan karawar su a rukunin D.
Ghana ta lallasa ƙasar Cape Verde wadda a wannan karon ne ta fara halartar gasar da ci 2-0.
Ita kuwa Kamaru ta fafata ne da ƙasar Mali, inda ta doke ta da ci 2-1. ‘Yar wasan Kamaru, Ngah Manga, ita ce ta zura ƙwallaye biyun da suka tabbatar wa Kamaru da nasara a wasan.
