Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya  gwamnonin jihohi da su daina gina gadoji  (flyovers) a wuraren da ba a buƙatarsu, maimakon haka su karkata kuɗaɗen wajen gudanar da ayyuka da samar da abubuwan da za su taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro da ke damun ƙasar.

Yayin da yake jawabi ga sarakunan gargajiya daga Jihar Oyo da suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ya kuma yi magana game da matsalar tsaro.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ke tsoratar da ‘Yan Najeriya ba ‘yan ƙasar ba ne, sannan ya ƙara da cewa matsalar tsaro a ƙasashe irinsu Mali, Burkina Faso, da Jamhuriyar Nijar na ƙara rurrumsa wutar ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

Tinubu ya shaida wa tawagar, wadda BaSaraken Ibadan (Olubadan of Ibadanland), Oba Rashidi Ladoja ya jagoranta, cewa kafa ‘Yan Sandan Jiha (State Police) zai zama gaskiya ba da daɗewa ba.

​Sannan ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta haɓaka tare da ƙarfafa masu gadin daji (forest guards) domin su tallafa wa ƙoƙarin sauran hukumomin tsaro.

​Ya bayyana cewa:​“A gaskiya, shi ya sa dole mu haɓaka ƙarfin masu gadin daji gami da kafa ‘yan sandan jiha, kuma kai ma ka taɓa yin gwamna a baya.

​“Ina buƙatar ka taimaka mana wajen isar da saƙo zuwa ga waɗannan gwamnonin. A yau, tsadar gudanar da ayyuka ta yi yawa. Amma kuɗaɗen da nake tura wa jihohi, da a ce ka same su a lokacin mulkinki ko a lokacina, da abin ya bambanta.

​“A yanzu babu mai cin bashin kuɗi domin biyan albashi. Masu murabus (pensioners) suna karɓar haƙƙinsu, kuma ya kamata jihohi su ƙara azama, maimakon gina gadajen sama a wuraren da babu cunkoson ababen hawa. Ya kamata su gina hanyoyi da rassa na sadarwa domin haɓaka ingancin rayuwa da kuma sauƙaƙa wa hukumomin tsaro damar shiga waɗancan yankuna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *