Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ya aike wa Kungiyar Masu Kamfanonin Jiragen Sama ta Kasa (AON) wata wasika game da shirin dakatar da zirga-zirga ko karin kudin tikiti, yana kira gare su da su kwantar da hankalinsu.
Wannan mataki ya biyo bayan kukan da kamfanonin suka yi ne cewa farashin man jirgi ya tashi da kashi 300 cikin dari, inda ya koma naira 3,300 kan kowace lita a maimakon naira 900 da ake sayarwa a watan Fabrairu.
Ministan ya roƙi kamfanonin jiragen da su janye shirin dakatar da aiki da za su fara a mako mai zuwa, yana mai cewa yin hakan zai taba tattalin arzikin kasa da tsaro.
- Tsadar man jirgi ta ta’azzara a Najeriya
- Kamfanin jirgin sama na KLM ya soke tashin jirage 160
- Ba wanda ba shi da abin fada — Shugaba Tinubu
“Ina tabbatar muku cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta damu da matsalolinku, kuma muna daukar matakan gaggawa don magance su.
“Ina kira a gare ku da ku nuna dauriya yayin da muke kokarin nemo mafita.” inji Keyamo.
A sakamakon matsalolin da suka dabaibaye harkar ta sufurin jiragen saman, Gwamnatin Tarayya ta ware ranar Laraba mai zuwa, domin ganawa da masu ruwa da tsaki a Abuja da nufin nemo mafita.
Gabanin hakan Gwamnatin ta bukaci kamfanonin su jingine shirin karin kudin tikiti a halin yanzu domin kar a takura wa masu tafiye-tafiye.
Rahotanni daga sassan Najeriya na nuni da yadda ake samun tsaikon tashi a kan lokaci, ko karin kudin tikitin jiragen, matsalar da masu ruwan ke dangantawa da tsadar man jirgi, wato Jet A1.