Kamfanin KLM ya soke kusan jirage 160 a fadin duniya a yau sakamakon kalubalen tattalin arziki da tsaro a Gabas ta Tsakiya.

Babban kamfanin sufurin jiragen sama na kasar Holland, KLM, ya sanar da dakatar da wani bangare na ayyukansa ranar Alhamis, inda ya soke zirga-zirgar jirage kusan 160 da aka tsara za su tashi a fadin duniya.

Matakin ya jefa dubun dubatar matafiya cikin rudani da rashin sanin makoma, musamman a babbar tashar jiragen saman dake Schipol na kasar Amsterdam, da kuma sauran sassan duniya.

Hukumar gudanarwar KLM ta ce wadannan matsaloli sun faru ne sakamakon wasu abubuwa guda uku da suka shafi harkar sufurin jiragen sama a duniya, cikin su kuwa har da tsadar man jirgi.

kamfanin ya ce rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da barazanar toshe hanyar ruwa ta Hormuz na daga cikin manyan dalilai.

KLM din ya ce ya dakatar da ratsa sararin samaniyar kasashen Iran da Iraki da Isra’ila saboda barzanar tsaro, lamarin da ya tilasta wa jiragen da ke zuwa yankin Asiya da kasashen Larabawa bin doguwar hanya.

Tsarin na bukatar karin yawan man da jirgin ke sha da kuma na lokacin aiki ga ma’aikatan sa, maimakon haka KLM din ya rage yawan zirga-zirga domin rage asarar kudaden gudanarwa.

Haka nan kamfanin ya ba da sanarwar dakatar da dukkan jiragen da ke zuwa Dubai, Riyadh da Dammam har zuwa ranar 31 ga watan Mayu, 2026. Soke jiragen na yau ya shafi sauran hanyoyin da har yanzu suke a bude amma masu hadari da tsada.

Masana harkokin sufurin jiragen sama na fargabar cewa idan rikicin gabas ta tsakiya bai lafa ba, manyan kamfanoni irinsu Lufthansa da Air France na iya bin sahun KLM.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *