Matsalar tabin hankali tsakanin matasa na ƙara zama babban abin damuwa a duniya, yayin da damuwa da baƙin ciki da wasu matsalolin tunani ke ƙaruwa.
Masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar na iya barin mummunan tasiri na dogon lokaci ga rayuwar matasa.
Matsin rayuwar zamani da amfani da kafafen sada zumunta da matsin karatu da kuma rashin tabbas na tattalin arziki na daga cikin abubuwan da ake dangantawa da ƙara tabarbarewar lafiyar kwakwalwa tsakanin matasa.
A cewar bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), baƙin ciki na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa nakasa tsakanin matasa, yayin da kashin kai ke cikin manyan abubuwan da ke haddasa mutuwar mutane masu shekaru tsakanin 15 zuwa 29.
Kafafen sada zumunta ma na taka rawa wajen ƙara matsalar.
Duk da cewa suna taimaka wa mutane wajen nishaɗi da amfani da su na iya jawo rashin yarda da kai da cin zarafi ta intanet da kuma yawan kwatanta rayuwar mutum da ta wasu.
- Ƙalubalen tsaro da sahihancin zaɓe a Osun
- INEC ta sake buga takardun zaɓen Osun domin saka ɗan takarar SDP
Wasu matasa kan ji matsin lamba na nuna cewa rayuwarsu tana tafiya cikin farin ciki da nasara a kafafen sada zumunta, yayin da a zahiri suke fama da matsaloli a ɓoye.
Barkewar cutar COVID-19 ma ta ƙara tsananta matsalar, musamman sakamakon zaman gida da rufe makarantu da warewar mutane.
Hakan ya sa wasu matasa suka fuskanci kaɗaici da damuwa, yayin da rashin samun damar zuwa wuraren ba da shawarwari kai tsaye ya sa wasu suka ci gaba da fama da matsalar ba tare da taimako ba.
Duk da ƙara wayar da kan jama’a, samun kulawar lafiyar kwakwalwa har yanzu na da wahala a wurare da dama. Tsoron abin da mutane za su ce ko kyamar masu fama da matsalar na hana wasu matasa neman taimako.
A wasu ƙasashe masu tasowa kuma, ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiyar kwakwalwa na ƙara dagula matsalar.
Masana sun nukaci gwamnati da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya su ba lafiyar kwakwalwar matasa muhimmanci, ta hanyar ƙara shirye-shiryen wayar da kai da kuma samar da damar samun shawarwari da kulawar ƙwararru.
Iyaye da masu kula da matasa ma na da muhimmiyar rawa wajen samar da yanayin da matashi zai iya bayyana matsalolinsa ba tare da tsoro ko kunyata ba.
Haka kuma, fasaha na iya taimakawa wajen samar da shawarwari ta intanet da wasu manhajojin da ke taimaka wa masu neman tallafin lafiyar kwakwalwa, ko da yake bai kamata su maye gurbin kulawar ƙwararru kai tsaye gaba ɗaya ba.
Lafiyar kwakwalwa tana da muhimmanci kamar lafiyar jiki. Don haka, yaƙi da wannan matsala na buƙatar haɗin gwiwar iyalai da makarantu da ma’aikatan lafiya da gwamnati da al’umma baki ɗaya.