Arsenal ta fara kare kambun Gasar Firimiyar Ingila da karfi bayan ta murkushe Coventry City da ci 3-0 a wasan bude kakar wasa na bana 2026/27 da suka buga a filin wasa na Emirates stadiya.

Tun da farko, ‘yan wasan na Gunners sun nuna cewa sun shirya komawa fagen wasa da karfi bayan doke Manchester City da suka yi da ci 3-0, a wasan Community Shield makon da ya gabata. Sannan kuma da wannan nasarar sun sake aika wani sako ga abokan hamayyarsu na gasar.

Kai Havertz, da Bukayo Saka da kuma kyaftin Martin Odegaard sune suka ciwa Arsenal kwallayen da suka bata nasara yayin karawar.

Da wannan nasara, a yanzu kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya yi nasarar lashe wasanni 150 a Gasar Firimiyar Ingila cikin wasanni kasa da 250 da ya jagoranta.

Wannan shine wasan Coventry na farko a Gasar Firimiyar Ingila tun 2001. Damarsu mafi kyau ta cin kwallo yayin fafatawar ta zo ne ta hannun Jack Rudoni, amma sai bugun ya je kai tsaye cikin hannun David Raya, mai tsaron ragar Arsenal.

’Yan wasan na Lampard suna bukatar sake inganta salon wasan su kafin su hadu da Hull City a wasa mai zuwa. Yayin da Arsenal za ta ziyarci Aston Villa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *