A yayin da za a fara Gasar Firimiyar Ingila a ranar Jumma’ah, 21 ga watan Augustan 2026, tambaya ɗaya da magoya ƙwallon ƙafa da kuma masu sharhi ke yi shine: ko ƙungiyar Arsenal za ta iya kare kambun da ta lashe a bara?
Kocin Arsenal, Mikel Arteta na burin lashe kofin gasar sau biyu a jere, to amma akwai buƙatar ya ƙara inganta salon ‘yan wasan gaban ƙungiyar domin cimma hakan.
Arsenal ta kawo ƙarshen dogon jiran lashe kofin Gasar Firimiya a kakar da ta gabata, inda ta lashe kofin a karon farko tun bayan shekara 22.
-
Galatasaray ta yi fatali da tayin Al-Hilal na yuro miliyan 150 akan Osimhen
-
Gasar Super Six: Yadda Plateau United da Mighty Jets suka yi nasara a wasan farko
-
Julián Álvarez ya shirya kakar wasa ta uku a Atlético Madrid
Wannan yana nufin za su fara wannan kakar ne a matsayin masu riƙe da kofin.
Kafin zuwan tsohon kocin Manchester City, Pep Guardiola Ingila, koca-kocai biyu ne kawai suka taɓa kare kofin a tarihin Gasar Firimiya, su ne Sir Alex Ferguson a Manchester United da Jose Mourinho a Chelsea, kuma City ce kawai ta taɓa kare kofin tun 2009.

Lokacin da Mikel Arteta ya zama kocin Arsenal, ya gabatar da ƙudiri 5 don cire ƙungiyar daga halin koma baya, inda ya ce yana son gina wata daula mai cike da tarihin nasarori.
Har zuwa wannan shekara, ƙungiyar na cikin mataki na 1 zuwa 4 na ƙokarin mayar da ita kamar zamanin Arsene Wenger domin lashe manyan kofuna.
Ƙungiyar Arsenal ba ta taɓa kare Gasar Firimiya ba tun bayan da Gunners din ta lashe kofuna 3 a jere wanda ya ƙare a shekarar 1935.
A cikin jawabin sa na baya-bayan nan, Arteta ya ce a yanzu ya mayar da hankali ne wajen kwaɗaitar da ‘yan wasan sa tunanin lashe Gasar Firmiya sau biyu a jere.
Nasara da ci 3-0 da Arsenal ta yi a kan Manchester City a wasan Community Shield, inda Arsenal ta mamaye wasan tun daga farko har zuwa ƙarshe ta lashe kofin, hakan ya nuna alamar ƙwarin gwiwar da ƙungiyar ke da shi don lashe kofin Firimiya sau biyu a jere.
Arsenal za ta buɗe wasan a kakar bana da ƙungiyar Coventry City ranar Jumma’a, 21 ga watan Augustan 2026 a filin wasa na Emirates da misalin karfe 8:00 na dare agogon Najeriya.