Ƙungiyar Plateau United da ta Mighty Jets dukkan su daga jihar Pilato, sun fara gasar NPFL Super 6 ta 2026 da ƙafar dama, yayin da suka doke takwatorinsu a wasannin rukuni na farko da suka buga a ranar Laraba, a sabon filin wasa dake Jos.
Plateau United ta doke Rivers United da ci 1–0, yayin da Mighty Jets ita ma ta samu nasara da ci 1–0 a kan El-Kanemi Warriors ta Maidugurin jihar Borno.
Plateau United ta fara wasan ne da ƙarfin ta a kan Rivers United, sai dai ƙungiyoyin biyu duka sun nuna ƙarfin hali da jajircewa yayin fafatawar.
Plateau United ta samu nasarar zura ƙwallon ta ne ta hannun Jibril Ibrahim, amma Rivers United ta yi ƙokarin farke ƙwallon, sai dai masu tsaron bayan Plateau United sun yi tsayuwar daka wajen kare gidan su, inda aka ta shi ci 1-0.
-
Julián Álvarez ya shirya kakar wasa ta uku a Atlético Madrid
-
Daga Najeriya zuwa Kamaru: Jerin cikakkun zakarun WAFCON
-
NFF ta sallami kocin tawagar Super Falcons
Kazalika, ita ma Mighty Jets ta ci ƙwallon ta ne ta hannun Usman Meyanga a minti na 56, bayan an tashi rabin farko na wasan babu ci tasakani, wato 0-0.
El-Kanemi Warriors sun yi ƙokarin matsawa Mighty Jets don farke ƙwallon sai dai haƙan su bai cimma ruwa ba.
Waɗannan sakamakon sun bai wa Plateau United da Mighty Jets ƙwarin gwiwa mai ƙarfi a gasar, yayin da Rivers United da El-Kanemi Warriors za su yi fatan farfaɗowa a wasannin su na gaba.
A cigaba da gasar, ga jadawalin wasannin da za a buga ranar Alhamis, 20 ga watan Augustan 2026.
Ranar Wasa ta 2 – Alhamis, 20 ga Agusta, 2026
Katsina United za ta kara da El-Kanemi Warriors, da misalin 2:00 na rana.
Rangers International za ta fafata da Rivers United, da misalin 4:00 na yamma.