Ba sabon labari ba ne yanzu cewa Kamaru ta zama zakarun Gasar Cin Kofin Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON) a karon farko, bayan ta doke Malawi da ci 3–0 a wasan ƙarshe na 2026 da aka buga a Rabat, dake Marokko.
Tawagar, wadda ake yi wa laƙabi da Indomitable Lionesses sun ajiye tarihi a ranar Lahadi, 16 ga Agusta, inda suka nuna ƙwazonsu a rabin farko na wasan yayin da suka zura ƙwallaye uku.
Marie Ngah Manga ta zura ƙwallaye biyu, yayin da Naomi Ndjoah Eto ta zura ɗaya, inda aka ta shi a wasan da ci 3–0. Wannan nasara ta kawo ƙarshen doguwar jira da Kamaru ta daɗe tana yi na lashe kofin nahiyar, bayan sun taɓa kaiwa wasan ƙarshe sau uku ba sa yin nasara.
-
NFF ta sallami kocin tawagar Super Falcons bayan ficewa daga Gasar WAFCON
-
Gusau ya ƙaddamar da kwamitin bincike na NFF
-
Galatasaray ta yi fatali da tayin Arsenal akan Victor Osimhen
Nasarar da Kamaru ta samu ta sanya yanzu an samu ƙasashe 4 a jerin zakarun WAFCON: Najeriya, da Equatorial Guinea, da Afirka ta Kudu da kuma Kamaru.
Yadda Najeriya ta yi fice a Gasar WAFCON
Har yanzu Najeriya ita ce ƙasar da ta fi samun nasara a tarihin Gasar WAFCON, inda ta lashe kofuna 10.
Najeriya ta lashe kofinta na ƙarshe a 2025, lokacin da Super Falcons ta farfaɗo daga baya ta doke ƙasar Marokko, mai masauƙin baƙi da ci 3–2 a wasan ƙarshe a Rabat.
Equatorial Guinea
Equatorial Guinea ita ce ƙasa ɗaya tilo banda Najeriya da ta taɓa lashe Gasar WAFCON sau biyu kafin nasarar Kamaru a 2026.
Equatorial Guinea ta ajiye tarihi a 2008 lokacin da ta doke Afirka ta Kudu da ci 2–1 a wasan ƙarshe a gida. Kafin nan, ta fitar da zakarun da ke rike da kofin, wato Najeriya, a wasan kusa da na ƙarshe.
Shekaru hudu bayan haka, Equatorial Guinea ta sake lashe kofin, yayin da ta doke Kamaru da ci 2–0 a wasan kusa da na ƙarshe, sannan ta doke Afirka ta Kudu da ci 4–0 a wasan ƙarshe.
Kofunansu biyu sun sanya Equatorial Guinea zama ƙasa ta biyu mafi nasara a tarihin WAFCON.
Afirka ta Kudu
Afirka ta Kudu ta kawo ƙarshen doguwar jira da ta daɗe tana yi don lashe kofin WAFCON a 2022.
Banyana Banyana sun taɓa kai wasan ƙarshe sau da dama ba tare da lashe kofin ba. Nasararsu ta zo ne a Marokko, inda suka doke mai masauƙin baƙin da ci 2–1 suka zama zakarun Afirka a karon farko.
Jerin Zakarun WAFCON:
- Najeriya – Kofuna 10 (1998, 2000, 2002, 2004, 2006, 2010, 2014, 2016, 2018 da kuma 2024)
- Equatorial Guinea – Kofuna 2 (2008 da kuma 2012)
- Afirka ta Kudu – Kofi 1 (2022)
- Kamaru – Kofi 1 (2026)
