Ayyoub Bouaddi, dan wasan Marokko da Lille.

Manchester City ta cimma yarjejeniya da Lille don sayan dan wasan tsakiya na kasar Marokko, Ayyoub Bouaddi, kan kudi har fam miliyan 86.

City za ta bayar da ruwan kuɗi da aka tabbatar fam miliyan 81.3, tare da biyan karin kudi fam miliyan 4.3 na cika wasu sharudda.

Dan wasan mai shekara 18 zai zama dan wasa mafi tsada da aka taba saya yana matashi a tarihin Gasar Firimiyar Ingila, inda zai wuce fam miliyan 58.9 da Manchester United ta amince ta biya Lille kan Leny Yoro a 2024.

Lille ta samu kudin da take nema a kan Bouaddi, wanda ya kasance daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi fice a Gasar Cin Kofin Duniya ta wannan bazara tare da Marokko.

City na kokarin sake gina tsakiyar gidanta bayan tafiyar Rodri, Bernardo Silva da Tijjani Reijnders.

Har ila yau, City ta nuna sha’awar sayan Enzo Fernandez na Chelsea da Manu Kone na Roma, duk dai domin sake gina tsakiyar gidanta.

Matashin dan wasan yana iya taka leda a matsayin dan wasan tsakiya mai kare gida, ko kuma a gaba kadan, wanda hakan zai kara baiwa City karin karfi.

Duk wanda ya bi diddigin yadda Marokko ta buga Gasar Cin Kofin Duniya kwanan nan tabbas zai san sunan Ayyoub Bouaddi. Yana daga cikin ‘yan wasan da suka ja hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *