Zakaran Gasar NPFL, Rangers International, za ta kara da mai masauƙin baki Plateau United a wasan ƙarshe na gasar shirye-shiryen kakar wasa ta NPFL Super 6 ta 2026 a sabon filin wasa na Jos, a ranar Lahadi, 23 ga Agusta.

Rangers, wadda ta lashe Gasar NPFL na kakar bara 2025/26 bayan ta doke Ikorodu City 2-1 a Lagos, za ta nemi tabbatar da cewa har yanzu ta na da ƙarfin ta kuma za ta iya kare kambun da ta lashe a bara.

A gefe guda kuma, Plateau United za ta yi amfani da yawan magoya bayan ta a sabon filin wasa na Jos.

United ta fara Gasar Super 6 da kyau, inda ta doke Rivers United da ci 1-0 a wasan su na farko, da ƙwallon da Jibril Ibrahim ya zura a raga.

Yayin da Rangers ke son nuna cewa har yanzu tana da tsari mai ƙarfi a Gasar Najeriya, Plateau United za ta yi amfani da fa’idar gida da kuma ƙwarin gwiwar da suka samu a gasar don lashe kofin.

An shirya Gasar Super 6 ne don baiwa ƙungiyoyin da suka halarta damar yin shirin fara Gasar NPFL ta bana da kyau, masu horas da ‘yan wasa kuma su samu damar gwada sababbin ’yan wasan da suka saya, da kuma gwada sabbin dabarun wasa kafin fara sabuwar kakar NPFL.

Haka kuma gasar tana da matuƙar muhimmanci ga ƙungiyoyin Najeriya da za su buga Gasar Zakarun Nahiyar Afirka da kuma Confederation cup.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *