Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya kare wata sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma kwanan nan, yana mai cewa ita ce hanya mafi dacewa da ƙasar za ta bi domin fita daga halin da ya bayyana a matsayin “ba yaƙi ba, ba zaman lafiya ba.”
A cikin wani jawabi da kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya wallafa da sanyin safiyar Lahadi, Pezeshkian ya ce mambobin Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran sun yi imanin cewa yarjejeniyar ita ce mafi kyawun yarjejeniya da za a iya samu, bisa mutunci da hikima da kuma muradun ƙasa.
Yarjejeniyar, wadda Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a kanta a watan Yuni, ta tanadi wa’adin kwanaki 60 domin kawo ƙarshen yaƙin da Iran, da kuma cimma matsaya kan shirin nukiliyar ƙasar.
- Tsohon Shugaban Kongo Kabila ya kalubalanci takunkumin da Amurka ta sa masa a kotu
- Kanada za ta sanya harajin kayayyaki kan Amurka
- Ba a sanar da halin da Paul Biya ke ciki a hukumance ba— Maisharhi
Sai dai wa’adin ya ƙare a makon da ya gabata, kuma har yanzu Amurka da Iran suna da babban saɓani.
Babu wata alama da ke nuna cewa ɓangarorin biyu sun cimma matsaya kan muhimmin batun sake buɗe mashigar ruwan Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar kayayyaki da man fetur a duniya.
Pezeshkian ya kuma danganta yarjejeniyar da makomar tattalin arzikin Iran, yana cewa ƙasar ba za ta iya jawo masu zuba jari ba matuƙar tana cikin wannan yanayi na rashin tabbas.
A gefe guda, sabon shugaban Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran Mohsen Rezaei, mai tsattsauran ra’ayi, ya gargadi ƙasashen da ke makwabtaka da Iran da kada su shiga sabon shirin Amurka na raunana tattalin arzikin Iran.
Rezaei ya ce Iran za ta iya kai hari kan hanyoyin jigilar man fetur daga Tekun Farisa, waɗanda ake amfani da su a matsayin madadin mashigar Hormuz, idan ƙasashen makwabta suka shiga abin da ya kira yaƙin tattalin arziki da ake yi wa Iran.