Gwamnatin Tarayya na daf da sake fasalta tsarin karatun aikin noma a kwalejojin kimiyya fasaha da a Najeriya.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, shi ne ya bayyana sabon shirin, ta hanyar gabatar da sabon tsarin karatu da zai fi mayar da hankali kan horarwa a aikace maimakon a rubuce.

Alausa, yace tsarin ya sha banban da tsohuwar hanyar da ake bi, ta karantarwa a ajujuwa ba tare da kwarewa a aikace ba, kuma an yi masa laƙabi da “wadata ɗalibai da ƙwarewa, sarrafa amfani da kasuwancin kayan noma” wato (agribusiness) a turance.

A ƙarƙashin tsarin, ɗalibi za iyi amfani da ƙwarewar sa nan take, wanda hakan ke nufin samar da masu takardar shaidar digiri da za su iya ƙirƙirar sana’o’I, domin samar da ayyukan yi maimakon dogaro gwamnati.

Sannan, shirin zai ƙarfafa horarwa a manyan fannonin noman abinci da kiwo, sarrafa amfanin gona, da kasuwancinsa.

Burin gwamnati inji ministan itace samar da sauyi a bangaren noma, domin dogaro da kai da samar ayyukan yi tsakanin matasa, domin bunkasar tattali arziki da rage yawan rashin aikin yi.

Kundin sabon tsarin zai kunshi kaso 20 na koyarwa a cikin aji, yayin da kaso 80 cikin  dari zai kasance a aikace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *