Shugaban kungiyar Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya musanta zargin cewa ba ya son Kiristoci, yana mai cewa zarge-zargen da ake yi masa ba su da tushe.
Sheik Jingir ya ce kalaman da ya yi a wajen bikin aurar da ma’aurata 1,500 da gwamnatin jihar Kano ta shirya, ba su kasance da nufin nuna kyama ga Kiristoci ko wadanda ba Musulmi ba.
Malamin ya fuskanci suka bayan wasu kalamansa da aka bayyana a matsayin masu rura rarrabuwar kawuna tsakanin addinai.
-
Tallafin Mai: Koma wa tsohon tsari zai ta’azzara matsalar tattalin arziki — Ministan Yaɗa Labarai,
-
Malaman Musulunci 500 sun amince da takarar Tinubu
Da yake magana a wani taron yini guda na kasa da aka gudanar a Jos ranar Lahadi, mai taken “shiga siyasa domin wanzar da adalci a matsayin mafita ga hadin kan kasa da ci gabanta”, Sheik Jingir ya ce ba ya nufin nuna kiyayya ga Kiristoci.
Hedikwatar JIBWIS ce ta shirya taron, domin wayar da kan mabiyanta kan muhimmancin shiga zabuka masu zuwa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da gwamnonin Yobe,da Kano, da Jigawa da Sokoto, na daga cikin wadanda suka halarci taron.
“Mutane da dama suna cewa ba na son Kiristoci, Karya ce kuma anyi wa kalamaina mummunar fassara. Shugabanci a Musulunci ba wai yaudarar mutane masu addinai daban-daban ba ne, Musulunci yana koyar da nuna kauna ga mutane masu addinai ko mazhabobi daban-daban.”Inji Shi
Ya kara da cewa Musulunci ya tanadi cewa duk Musulmin da ya zalunci ko ya yaudari wanda ba Musulmi ba, za a tambaye shi a ranar kiyama, domin Annabi Muhammad (SAW) ya zauna lafiya da wadanda ba Musulmi ba.
Malamin ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin jihohi da sauran shugabanni da su yi adalci ga kowa, ba tare da la’akari da kabila ko addini ko banbancin siyasa ba.
Ya kuma jaddada cewa, kowane dan Najeriya na da ‘yancin zabar dan takarar da yake ganin ya dace da shi a lokacin zabe.
Sai dai malamin ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, da hadin kai da zama tare, yana mai cewa babu ci gaba idan babu zaman lafiya.