Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken garambawul a harkar ƙwallon ƙafa ta ƙasar domin shawo kan matsalar rashin samun tikitin shiga manyan gasannin yanki, na nahiyar Afirka da kuma na duniya.
A cikin wata sanarwa da Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Alhamis, Shugaba Tinubu ya ce gyaran zai mayar da hankali ne wajen ƙarfafa shugabanci, gudanarwa, wakilcin masu ruwa da tsaki, bunƙasa ’yan wasa, gasa ta cikin gida da kuma tabbatar da riƙon amana a harkar ƙwallon ƙafa.
Sanarwar ta ce shugaban ya lura cewa yayin da sauran wasanni suka samu ci gaba tun bayan sake fasalin fannin wasanni ƙarƙashin Hukumar Wasanni ta Ƙasa, ƙwallon ƙafa ta ci gaba da fuskantar matsaloli saboda raunin tsarin gudanarwa.
- Yan Najeriya 67 sun dawo daga Afirika ta Kudu
- Ban goyi bayan gayyatar VeryDarkMan taron lauyoyi na kasa ba-Falana
- Hare-haren Borgu: Majalisar koli ta addinin Musulunci ta bukaci a dauki matakin gaggawa
Tinubu ya ce ƙwallon ƙafa, wadda ita ce wasa mafi shahara a Najeriya kuma wadda ta fi samun tallafi, jari da kulawar ƙasa, tana ci gaba da fama da matsaloli ne sakamakon gibin da ke cikin tsarin tafiyar da harkar.
Shugaban ya jaddada cewa dole ne ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta dace da irin baiwar ’yan wasa, ƙauna da albarkatun da ƙasar ke da su, ta hanyar samar da ƙungiyoyi masu ƙarfi da kuma ci gaba mai ɗorewa.
Ya kuma umurci Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa da ya yi aiki tare da Sakatariyar Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa tare da samar da tsarin gyara.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a gudanar da tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF), tare da tabbatar da cewa Najeriya ta kiyaye dukkan wajibanta a tsarin ƙwallon ƙafa na duniya.
Shugaba Tinubu ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da ’yan Najeriya su goyi bayan wannan sauyi domin gina tsarin ƙwallon ƙafa mai ƙarfi, mai gaskiya da kuma samun nasara.
Hakan dai na zuwa ne sao’i kadan bayan shugaban hukumar kula da wasanni ta Najeriya Ibrahim Musa Gusau ya ajiye aiki da hukumar biyo bayan fuskantar matsin lamba da harkar kwallon kafa ke fuskanta a kasa.