Abubuwan da sojoji suka kwato a Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato

Dakarun sojin (Rundunar Oeperation Enduring Peace) sun hallaka wani wanda ake zargin ɗan ta’adda ne tare da ƙwato makamai a ƙauyen Zak dake Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.

Wannan na ɗauke ne a cikin wata sanarwa da Jami’in yaɗa labarai na rundunar, kyaftin Chinonso Polycarp, ya fitar ranar Lahadi, 30 ga watan Augustan 2026.

A cewar sanarwar, dakarun sojin sun gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri yayin da su ka yi ƙoƙarin tsayar da wata mota ƙirar Golf mai launin shuɗi ɗauke da Lamba mai DKA-808-XM domin gudanar da bincike.

Sanarwar ta ce bayan dakatar da motar, yunƙurin gudanar da binciken motar ke da wuya sai direban motar ya sauka daga motar, inda yayi ƙoƙarin guduwa amma sojojin sun bi shi, inda su ka kamo shi, amma direban ya yi ƙoƙarin ƙwace bindiga daga hannun wani soja nan take aka hallaka sa.

Abubuwan da aka ƙwato bayan gudanar da bincike a cikin motar sun haɗa da bindiga ƙirar AK 47 guda biyu, da kwanson bindiga, da bindigogi biyu masu hannun katako da sauransu.

Kwamandan (Rundunar Operation Eduring Peace), Manjo-Janar Maxwell Dangana, ya yabawa dakarun kan jajircewar su wajen yaƙar ’yan ta’adda a fadin wuraren da suke gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya, inda ya buƙace su da su ci gaba akan hakan.

Har ila yau, Kwamandan ya yabawa al’umma akan goyon bayan da suke baiwa dakarun soji, yayin da ya ƙara yin kira da su ƙara ƙaimi wajen bayar da bayanan sirri don daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *