Dakarun haɗin gwiwa na Operation FANSAN YAMMA sun samu kama mutane uku da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda, tare da ƙwace makamai da alburusai, da kuma lalata maboyar ’yan ta’adda.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar, ya ce an gudanar da ayyukan ne a ranakun 27 da 28 ga Agusta, 2026, a wasu wurare daban-daban na jihohin Kaduna da Katsina.
Ya ce a ranar 27 ga Agusta, dakarun sashe na 1 sun samu bayanan sirri kan wani mutum da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda a Jihar Kaduna.
- ‘Yan sanda sun ceto mata biyu ‘yan Colombia da aka yi garkuwa da su a Legas
- Mallakar makamai ba bisa ka’ida ba: Kotu ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kwanaki 250 a gidan gyaran hali
- Rundunar ’yan sanda ta jihar Neja ta kama mutane 6 da ake zargi da sace mutane
A cewar sanarwar, jami’an sun kama wanda ake zargin da bindigogi guda biyu da aka ƙera a gida, da kuma alburusai 13, waɗanda aka ɓoye a cikin wata jaka.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya samu umarnin kai makaman da alburusai ga wani mutum.
Bayan samun wannan bayani, dakarun sun gudanar da wani samame na gaggawa, inda suka kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen safarar makaman.
A halin yanzu, mutanen ukun suna hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike, tare da makaman, alburusai da sauran kayayyakin da aka kwato.
A wani samame da aka gudanar a ranar 28 ga Agusta, dakarun sashe na 2, tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro, sun kai farmaki kan wasu maboyar ’yan ta’adda da aka gano a yankunan Maharba da Karaduwa, cikin ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Dakarun sun yi nasarar share yankunan tare da lalata maboyar da kuma wasu gine-ginen da ake zargin ’yan ta’addan na amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Sanarwar ta ce dakarun sun kuma lalata wata maboya da ke da alaƙa da fitaccen shugaban ’yan ta’adda, Kachalla Muhammadu Filani, wanda ake zargi da jagorantar ƙungiyar da ke addabar fararen hula a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa.
Rahoton ya ce Kachalla Muhammadu Filani ya tsere da ƙyar yayin da dakarun ke matsowa kusa da maboyarsa.
A yayin ci gaba da binciken yankin, dakarun sun kwato bututun RPG-7, babur, wayoyin hannu da wasu kayayyaki.
Bayan haka, dakarun sun ci gaba da gudanar da sintiri da ayyukan yaƙi a yankin domin ƙarfafa nasarorin da aka samu da kuma hana ’yan ta’addan samun damar gudanar da ayyukansu.