Shugaba Bola Tinubu ya shigar da ƙara a gaban kotun Amurka domin hana Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, da Hukumar FBI da Kuma DEA fitar da takardu da suka shafi zarginsa da safarar miyagun ƙwayoyi.
Wani ɗan gwagwarmayar neman kare hakkin ɗan Adam ɗan kasar Amurka, Aaron Greenspan, ne ke neman waɗannan takardu.
Greenspan ya shigar da ƙara inda ya yi amfani da dokar ‘Yancin Samun Bayanai, ta (FOIA), a kan wasu hukumomin gwamnatin Amurka don neman takardun da suka shafi binciken da aka yi wa Tinubu.
-
Zan dawo da kasashen AES cikin Ecowas – Atiku
-
‘Yan sanda sun ceto mata biyu ‘yan Colombia da aka yi garkuwa da su a Legas
-
Sojoji na yunkurin kifar da gwamnatin sojin Nijar
A cikin buƙatun Greenspan akwai cikakken fayil ɗin FBI kan Tinubu, da kuma takardun tambayoyi na FBI 302 da suka shafi lokacin tsakanin 1992 zuwa 1993.
Ƙarar ta kuma shafi wata takarda da ke da alaƙa da wata shari’ar kwace dukiya da aka yi a Amurka a shekarar 1993, wadda ta shafi kusan dalar Amurka 460,000 da ake dangantawa da Tinubu.
Sai dai Tinubu ya musanta aikata dukkan laifukan da ake zarginsa da yi.
A cewar takardun da lauyoyinsa, Christopher W. Carmichael, da Victor P. Henderson da kuma Oluwole O. Afolabi, suka miƙa wa manema labarai ranar Asabar, Tinubu ya yi zargin cewa idan aka fitar da waɗannan takardu tamkar an yi masa kutse ne a cikin ‘yancinsa.
