Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC Atiku Abubakar ya zargi shugaba Bola Tinubu da haddasa taɓarɓarewar tsaro a Yammacin Africa.

A wata tattaunawa da yayi da BBC Hausa, Atiku ya ce tsaron yankin ya kara taɓarɓarewa ne bayan da ƙasashen Nijar Mali da Burkina Faso SUKA fice daga ƙungiyar ECOWAS

Sai sai Aiku ya ɗora alhakin ficewar ƙasashen da ake kira AES  kan Shugaba Tinubu wanda shi ne shugaban ƙungiyar ta Ecowas a lokacin da aka yi taƙaddamar.

A cewarsa “Ban ga dalilin da ya sa Najeriya za ta ce ba za ta yi hulɗa da Nijar ba saboda an samu juyin mulki, Nijar da Najeriya al’umma ɗaya ne. Domin sojojin sun karɓi mulki bai kamata a sallami Nijar daga Ecowas ba.

Yayi bayanin cewa zai tabbatar da ganin an samu fahimtar juna tare da dawo da Nijar da Burkina Faso da Mali cikin Ecowas

Da yake Magana kan hanyar da zaibi don dawo da kasashen na AES cikin ECOWAS zai zauna da shugabannin ECOMOG domin tabbatar da an samu zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *