Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (ADC), Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sake buɗe iyakokin Najeriya da ƙasashen makwabta, tare da haɓaka tashoshin jiragen ruwa da ke yankin Kudu idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Atiku ya ce rufe iyakokin ya yi illa ga harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya da ƙasashen dake makwaftaka da ita, tare da ƙara yawan rashin aikin yi, musamman tsakanin matasan da ke dogaro da kasuwancin ketare domin samun abin dogaro da kai.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayanin shirinsa na magance matsalar rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma tsadar safarar kayayyaki a faɗin ƙasar.

Ya ce jihohin Arewa suna da iyaka da Kamaru, Chadi, Nijar da Jamhuriyar Benin, lamarin da ya sa kasuwancin tsakanin ƙasashe ya kasance wani muhimmin ɓangare na tattalin arzikin yankin.

Atiku ya kuma yi alkawarin inganta ababen more rayuwa na tashoshin jiragen ruwa a kudancin ƙasar domin sauƙaƙa jigilar kayayyaki da kuma samar da daidaitaccen tsarin sufuri.

Ya ce a baya ya nemi hanyoyin bunƙasa tashoshin jiragen ruwa a yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, ta hanyar tattaunawa da masu jigilar kayayyaki na ƙasa da ƙasa da kuma kamfanonin da ke haɓaka tashoshin jiragen ruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *