Ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar (ADC), Ambasada Omar Suleiman, ya yi watsi da wata sanarwa da aka danganta ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wadda ta amince da Alhaji Modibbo a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ADC na zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Yayin wani taron manema labarai a Yola, Sulaiman ya dage cewa shi ne halastaccen ɗan takarar gwamna da jam’iyyar ta zaɓa, yana mai cewa tuni an kai batun gaban Babbar Kotun Tarayya (Federal High Court).
Ya ce an gudanar da zaɓen fidda gwani na ADC ne ƙarƙashin sa-idon Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), inda ya yi nasara a kan Modibbo.
- Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’addan Boko Haram 21, Sun Lalata Sansaninsu a Adamawa
- Tinubu ya umurci a yi cikakken garambawul a harkar ƙwallon ƙafa ta Najeriya
- Yan Najeriya 67 sun dawo daga Afirika ta Kudu
A cewarsa, daga bisani an miƙa sunansa ga INEC a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar.
Suleiman ya ce ya garzaya Babbar Kotun Tarayya domin ƙalubalantar duk wani yunƙuri na sauya sunansa da wani, inda ya ƙara da cewa an miƙa takardun shari’a ga INEC da kuma jam’iyyar ADC a matakin ƙasa da jiha.
Ya yi kira ga Atiku da ya janye sanarwar da aka ce ya yi, tare da kaurace wa duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga tsarin shari’ar da ke gudana.
Suleiman ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar ADC da magoya bayanta a Adamawa da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa zai ci gaba da kare wa’adinsa ta hanyoyin da suka dace da doka da tsarin dimokuraɗiyya.