A wani mataki na ƙara ɗaga daraja da ƙarfin sojojin Najeriya wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, an kammala taron haɗin gwiwa a bangaren zamanantar da masana’antu kera makamai da kasuwancin su tsakanin Najeriya da Turkiyya karo na 7 a birnin Tarayya Abuja.

Turkiyyar, tace ba kawai sayar wa Najeriya makamai ne taron zai kalla ba, sabunta yarjejeniyar buɗe ƙofar musayar fasaha domin tallafa wa masana’antar ƙera makamai ta Najeriya (DICON) da ke Kaduna, domin fara ƙera wasu kayan yaƙi na zamani a gida.

Mataimakin Sakataren masana’antun ƙera makamai na ƙasar Turkiyya, Gökhan Uçar,  ya jagoranci wata tawagar masu ruwa da tsakin ƙasar zuwa taron, wanda ya haɗa manyan jami’an tsaro, masana, da ‘yan kasuwa daga masana’antun ƙera makamai na ƙasashen biyu.

Masu ruwa da tsaki daga Najeriya da Turkiyya [Hoto:DHQ]
A yayin taron, Turkiyya ta jaddada aniyar ci gaba da baiwa Najeriya goyon baya domin gina masana’antar ƙera makamai ta zamani, domin dogaro da kai wajen ƙera kayan yaƙi da duniya ke amfani da su a zamanance.

Haka nan Turkiyyar, tace ba kawai sayar wa Najeriya makamai ne taron zai kalla ba, sabunta yarjejeniyar buɗe ƙofar musayar fasaha domin tallafa wa masana’antar ƙera makamai ta Najeriya (DICON) da ke Kaduna, domin fara ƙera wasu kayan yaƙi na zamani a gida.

Haɗin kan ya sake tabbatar da amfani da fasahar zamani ta Turkiyya, wadda sojin saman Najeriya ke amfani da ita wajen gano maɓoya da murƙushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Sakamakon haɗin kan, Rundunar Sojin ruwan Najeriya ta karɓi sabbin jiragen yaƙi daga Turkiyya, domin amfani da su a yankin Naija Delta mai arziƙin manfetur, tare da samar wa sojojin ƙasa motocin yaƙi masu sulke da nakiya bata iya ratsa su.

Matakin, ya biyo bayan ƙarfafa dangantakar diplomasiyya da tsaro tsakanin Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya da shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu, da nufin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya, tsaro da daidaito a yankin yammacin Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *