Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta hannun jami’anta na ofishin INTERPOL na ƙasa da ke Legas, ta ceto mata biyu ‘yan ƙasar Colombia da ake zargin wata ƙungiya ta masu safarar mutane ta yaudaresu zuwa Najeriya tare da tsare su.
Rundunar ’yan sandan ta ce an ceto su ne a ranar Laraba, 26 ga watan Agustan 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da ofishin INTERPOL na ƙasa a Bogota ya bayar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda, CSP Ani Iniedu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
-
Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’addan Boko Haram 21, Sun Lalata Sansaninsu a Adamawa
-
An kammala taro kan tsaro tsakanin Najeriya da Turkiyya
-
Hare-haren Borgu: Majalisar koli ta addinin Musulunci ta bukaci a dauki matakin gaggawa
A cewar sanarwar, an “yaudari” matan biyu ne da ƙarfi suka kawo su Najeriya, aka tsare su ba da yardarsu ba, tare da ƙwace musu takardun tafiyarsu. Wasu ‘yan ƙasar Sin ne ake zargi da aikata hakan, amma a halin yanzu sun tsere.
Sanarwar ta ce bayan samun bayanan sirrin ne, ‘yan sanda suka fara gudanar da bincike na sirri, inda jami’an suka gano inda ake tsare da waɗanda abin ya shafa a Legas, sannan suka ceto su “a ranar da lamarin ya faru.”
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin sun tsere ne daga wajen sailin da suka ga zuwan ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun ce a yanzu haka ana riƙe da ‘yan Colombia ɗin biyu a wuri mai tsaro kuma ana ba su dukkanin kulawar da ya dace.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ofishin jakadancin Colombia da ke Accra na ƙasar Ghana na aiki tare da ofishin INTERPOL na ƙasa domin samun sauƙin komawar matan zuwa ƙasarsu.