Mazauna birnin Niamey, babban birnin Nijar, sun ce sun ji ƙarar harbe-harbe cikin dare a ranar Asabar, a kusa da wani sansanin sojoji da ke filin jirgin saman ƙasa da ƙasa, wanda mayaƙan ƙungiyoyin jihadi suka kai wa hari sau biyu a bana.

“An yi ta harbe-harbe mai ƙarfi da fashe-fashe a Sansanin 101 da ke Niamey,” wani mazaunin yankin ya shaida wa AFP, inda wasu shaidu da dama suka tabbatar da faruwar lamarin.

Wasu wallafe-wallafe a kafafen sada zumunta sun kuma bayar da rahoton jin harbe-harbe da fashe-fashe a sassa daban-daban na birnin, musamman a yankin gwamnati da fadar shugaban ƙasa da gidan talabijin na ƙasa suke.

Wasu bidiyoyi da aka wallafa a intanet sun nuna motocin sulke da aka tura domin ƙarfafa tsaro a yankin da ke kusa da filin jirgin saman.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin harbe-harben ba, kuma hukumomin Nijar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Filin jirgin saman Niamey ya fuskanci hare-haren ƙungiyoyin jihadi sau biyu a bana. Na farko ya faru ne a watan Janairu, inda ake zargin kingiyar EIS da kai harin, yayin da a ƙarshen watan Yuni kuma ƙungiyar kungiyar JNIM, reshen Al-Qaeda a yankin Sahel, ta sake kai hari.

Ƙungiyoyin jihadi biyu masu hamayya ba wai kawai suna kai hare-hare kan fararen hula da sojoji ba ne, har ila yau suna fafatawa da juna domin samun rinjaye a yankin Sahel, musamman a Nijar.

Hukumomi sun ce a harin da aka kai a watan Janairu, an kashe maharan 20, yayin da sojoji huɗu suka samu raunuka.

Janar Abdourahamane Tiani, shugaban gwamnatin sojin da ta hau mulki bayan juyin mulkin watan Yulin 2023, ya bayyana a watan Janairu cewa akwai “gibi a cikin tsarin tsaro” da ya ba da damar kai harin.

A cewarsa, manufar harin ita ce “lalata dukkan ƙarfin sojin sama” na rundunar sojin ƙasar.

A watan Yuni kuma, Ma’aikatar Tsaron Nijar ta ce an kashe aƙalla sojoji 11 da fararen hula biyu, yayin da aka kashe maharan 22. Rundunar sojin ƙasar ta ce ta samu nasarar fatattakar hare-haren biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *