Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya ce majalisar na buƙatar ƙarin dala biliyan 1.1 domin yaƙi da cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

Ya ce shirin Majalissar Ɗinkin Duniya na yaƙi da cutar, wanda ya kai dala biliyan 2.13, ya samu kaso 48 cikin 100 ne kawai na kuɗin da ake buƙata.

Guterres, ya ce tallafin da ake samu ya gaza matuka bisa la’akari da girman matsalar da ake fuskanta, ya yi gargadin cewa idan ba a samu ƙarin kuɗi cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar muhimman ayyukan yaƙi da cutar na iya rasa kuɗaɗe a daidai lokacin da ake buƙatar faɗaɗa su.

A cewar jami’ai, ɓarkewar cutar a gabashin Congo na yaɗuwa cikin yanayi mai matuƙar wahala, sakamakon rashin tsaro da ƙauracewar jama’a daga gidajensu, yajin aikin ma’aikatan lafiya da kuma yawan zirga-zirgar mutane daga wani wuri zuwa wani.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce har yanzu ba a samu nasarar shawo kan ɓarkewar cutar ba, inda ta yi gargadin cewa adadin masu kamuwa da cutar na iya zarce na ɓarkewar Ebola da ta auku a ƙasashen Yammacin Afirka tsakanin 2014 zuwa 2016, wadda ta fi kowace rasa rayuka, inda sama da mutum 11,000 suka mutu.

Ko da yake an bayyana ɓarkewar cutar a hukumance a tsakiyar watan Mayu, jami’ai sun yi imanin cewa ta fara yaɗuwa ne tun watan Fabrairu, daga baya ta yaɗu daga yankuna uku zuwa kusan 60, yayin da mafi yawan masu kamuwa da cutar da waɗanda suka mutu ba sa cikin jerin mutanen da hukumomi ke sa ido a kansu, lamarin da ke ƙara wahalar gano masu ɗauke da cutar.

Wata babbar matsala ita ce nau’in ƙwayar cutar da ke haddasa wannan ɓarkewar, wato Bundibugyo virus, wanda ba ta da ingantacciyar allurar rigakafi ko maganin da aka amince da amfani da shi a yanzu. Sai dai an fara gwaje-gwajen wasu allurai da magunguna a yankunan da cutar ta ƙamari, domin duba yiwuwar amfani da su wajen dakile ta.

Matakan da hukumomi ke ɗauka domin shawo kan cutar, ciki har da takaita tarukan jama’a, nisantar juna da kuma rufe wasu filayen jiragen sama, sun kawo cikas ga rayuwar al’ummomin da ke cikin larduna shida da cutar ta shafa. Lardin Ituri na daga cikin wuraren da lamarin ya fi tsanani, saboda rikicin ‘yan tawaye da ya daɗe yana addabar yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *