Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja ta ce ta kama mutane shida da ake zargi da alaƙa da wata ƙungiyar masu sace mutane da ke aiki tsakanin jihohi, musamman a yankunan Suleja da Kontagora, tare da alaƙa da jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda (PPRO), SP Wasiu Abiodun, ya fitar, rundunar ta ce ana zargin waɗannan mutanen da amfani da motoci masu zaman kansu wajen rage wa fasinjojin da ba su sani ba hanya, sannan su sa musu ƙwaya ko magani da zai sa su suma, kafin su sace su zuwa maboyarsu a jihohin makwabta.
Rundunar ta ce binciken ya biyo bayan sace wata mata da jaririnta a Suleja a ranar 7 ga Fabrairu, 2026.
- Iyakokin Najeriya a buɗe suke, Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar wa Atiku martani
- Abin da ya kamata ku sani game da sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
- NCC ta bukaci a zuba jari a sabbin hanyoyin fasaha na cikin gida
A cewar ’yan sandan, masu garkuwa da mutanen sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 50, sannan suka karɓi Naira miliyan 9.5, kafin matar ta samu damar tserewa.
An kuma bayyana cewa daga baya waɗanda ake zargin sun yi amfani da wayar hannu da katin ATM da matar ta bari domin neman ƙarin Naira miliyan 10.5 daga wata mata da aka sace a Shagari, Jihar Sokoto, yayin da take tafiya zuwa Kontagora.
An kama waɗanda ake zargin ne tsakanin Yuli da Agusta 2026. ’Yan sanda sun ce an kuma kwato wasu kayan tsafe-tsafe da sauran kayan tsafi daga hannun Abdullahi Sani a Zaria, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shirya sace wasu daga cikin mutanen da yake hulɗa da su ta hannun wani da ake zargin jagoran ƙungiyar ne mai suna Mustapha Yusuf.
A halin yanzu, Mustapha Yusuf, Jafar da Fatima suna nan a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo, yayin da sauran mutane shida da aka kama suke hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Rundunar ta shawarci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan, tare da bayar da sahihin bayani ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen dakile ayyukan masu garkuwa da mutane.