Masarautar Saudiyya ta kashe mutum 96 tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 22 ga watan Yunin 2026, inda 61 daga cikinsu suka shafi laifukan da suka hada da miyagun ƙwayoyi, a cewar wani rahoton kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International (AI).
An gudanar da kisan ne a daidai lokacin da Saudiyya ke ci gaba da amfani da hukuncin kisa a kan laifukan miyagun ƙwayoyi, ciki har da na ‘yan ƙasashen waje.
Daga cikin 61 da aka kashe kan laifin miyagun ƙwayoyi, 39 ‘yan ƙasashen waje ne.
Kungiyar ta kuma ce Saudiyya ta kashe mutum 356 a shekarar 2025, wanda shine mafi girma a shekara guda. Laifukan miyagun ƙwayoyi sun kai 240 daga cikin kisan, inda lamarin ya shafi ‘yan ƙasashen waje 188.
- Sojoji na yunkurin kifar da gwamnatin sojin Nijar
- ‘Yan sanda sun ceto mata biyu ‘yan Colombia da aka yi garkuwa da su a Legas
- Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’addan Boko Haram 21, Sun Lalata Sansaninsu a Adamawa
A wani labarin baya-bayan nan, hukumomin Saudiyya sun sanar da kashe wani ɗan Najeriya mai suna Idris Ibrahim, bayan an same shi da laifin safarar hodar ibilis cikin Masarautar. Ma’aikatar Cikin Gida ta Saudiyya ta ce an kashe Ibrahim ne a yankin Madina a ranar 24 ga watan Agusta.
Ma’aikatar ta bayyana cewa hukumomin tsaro ne suka kama shi da laifin safarar hodar ibilis, sannan bayan an kammala bincike aka gurfanar da shi a gaban kotu, yayin da Kotun ta same shi da laifi sannan ta yanke masa hukuncin kisa.
Ma’aikatar Cikin Gida ta Saudiyya na ganin hukuncin kisa ya zama dole domin yaki da safar miyagun ƙwayoyi da kuma kare rayuwar ‘yan ƙasa da mazauna kasar daga illolin miyagun kwayoyi.
Bayan kisan Ibrahim, ma’aikatar ta yi gargadin cewa duk wanda ya shiga harkar safarar miyagun ƙwayoyi zai fuskanci matsanancin hukunci. Amma ba ta bayyana yawan hodar ibilis da aka kama shi ba, ko kuma lokacin da aka kama shi da inda aka kama shi.