Shugaba Bola Tinubu na Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya fara hutu na makonni uku da ya saba yi na shekara-shekara.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu zai bar Abuja a yau Lahadi, inda zai wuce Nahiyar Turai kuma zai fara sauka ne a birnin Landon da ke ƙasar Birtaniya.

Onanuga ya ƙara da cewa, bayan kammala hutun, ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo gida domin shiga harkokin yaƙin neman zabe na watan Janairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *