Sojojin Rundunar Birged ta 17, ƙarƙashin Operation FANSAN YAMMA, sun kashe wasu manyan kwamandojin ’yan ta’adda biyu yayin wani samame da suka gudanar a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
An bayyana kwamandojin da aka kashe da sunayen Hamisu, wanda aka fi sani da Mamiyo, wanda ake zargi da safarar makamai kuma shi ne mataimakin Kachalla Muhammadu Fulani, da kuma Umar Bocho, wanda ke cikin manyan mataimakan ƙungiyar.
- Gobara ta laƙume kayayyakin miliyoi nairori a kasuwar Jabi dake Abuja
- Shugaba Tinubu ya fara hutun makonni uku, ya tashi zuwa Turai
- Dakarun soji sun hallaka wani ɗan ta’adda, sun ƙwato bindigogi a Jihar Filato
Rundunar sojin ta ce Kachalla Muhammadu Fulani ya tsere daga wurin yayin samamen, amma ya samu munanan raunukan harbin bindiga.
Sojojin sun kuma kwato tare da lalata babura guda biyu mallakar ’yan ta’addan.
Rundunar ta ce aikin wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin jami’an tsaro na tarwatsa hanyoyin sadarwa da ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Yamma.