Shugaban Hukumar yaki da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa an kori ma’aikatan hukumar sama da 40 sabo da laifukan cin hanci, rashawa, da maguɗin kuɗaɗe a tsawon shekaru uku da suka gabatOlukoyede ya kammala da cewa dole ne ka tabbata hannayen ka a tsaftace suke, domin ba za ka iya yaki da cin hanci da rashawa ba alhalin naka hannuwan suna gurbace.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a hedikwatar EFCC da ke Abuja, yayin wani taron manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu a karkashin shugabancin sa, inda ya ce yanzu haka ma’aikata biyar na gaban kuliya.

“A tsawon shekaru biyu da rabi zuwa shekaru uku da na yi ina aiki, na sa an kori ma’aikata sama da 40 saboda laifukan cin hanci da rashawa da kuma rashin gaskiya wajen gudanar da kuɗaɗe, yayin da a yanzu haka, aka gurfanar da fiye da mutum biyar daga cikinsu a kotu,” in ji Olukoyede.

Olukoyede ya bayyana cewa hukumar ta sauya wa tsangayar kula da al’amuran cikin gida suna zuwa tsangayar da’a da rikon amana wato (Department of Ethics and Integrity).

Ya bayyana cewa an yi wannan sauyi ne domin nuna jajircewar hukumar wajen fara tsaftace kanta daga cikin gida.

Shugaban ya bayyana cewa EFCC ta amince da sabuwar manufar karbar kyautuka ga jami’anta domin karfafa musu gwiwa akan gaskiya da rikon amana.

A karkashin manufar, jami’an hukumar za su rika bayyana kadarori da kyautukan da suka wuce adadin da aka kayyade, gami da wadanda suke samu daga ‘yan uwa daga kasashen waje.

Olukoyede ya kammala da cewa: “Dole ne ka tabbata hannayen ka a tsaftace suke, domin ba za ka iya yaki da cin hanci da rashawa ba alhalin naka hannuwan suna gurbace’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *