Mutanen da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta rusa gidajen su a karshen watan Mayun 2026 a birnin Yamai, za su dara, bayan da a wannan Litinin aka nuna masu wasu sabbin gidajen da za a rarraba wa rukunkin farko na wadanda abin ya shafa.
- An dawo da zaman lafiya a Niamey bayan yunkurin tawaye a rundunar sojin Nijar
- Nepal: An fara aikin ceto ma’aikata 933 da ake zargin ambaliyar ruwa ta binne
- An kashe mutum 96 a Saudiyya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni, ciki har da ɗan Najeriya.
Shafin Fitilar Nijar ya ruwaito cewa Ministan fasalta birane Maj. Kanal Abdoulakrim Amadou Daouda da mukarrban kwamitin da gwamnati ta kafa kan wannan lamari sun ziyarci unguwar mai sunan Cité de la Refondation da ke wajejen kauyen Soray mafitar birnin Yamai kan hanyar Dosso.
Daruruwan mutane ne aka rusa wa gidaje ko a ka kwace wa filaye a kewayen filin jirgin saman Yamai saboda dalilan tsaro a cewar mahukunta bayan hare-haren ta’addancin da aka kai filin jirgin na Yamai da sansanin Sojan sama 101 a watannin janeru da Yunin 2026.