Babban Sakataren rikon kwarya na Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya, (NFF) Dokta Emmanuel Ikpeme, ya bukaci tawagar ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya, Falconets, su bayar da mafi kyawun ƙoƙarinsu wajen doke ƙasar Koriya a wasan sada zumunta da za su buga a ranar Talata.
Ikpeme ya ja hankalin ‘yam matan da su maimaita irin kokarin da suka yi na doke kasar Poland mai masaukin baki a wani wasan sada zumunta da suka buga a ranar Juma’a.
Mary Mamudu ce ta ci kwallan da ta bai wa Falcnets nasara a karshen rabin farko a filin wasa na Municipal Stadiya dake Brzeg.
- Arsenal ta doke Aston Villa a Gasar Premier
- Enugu Rangers ta tashi 1-1 da Katsina United, Barau FC 3-1 Nasarawa United…
- Chelsea ta doke Brighton da ci 4-3
Falconets za ta buga wasanta na karshe na shirye-shiryen halartar Gasar Duniya a filin wasa na Remes Sports Leisure and Spa Stadiya a ranar Talata, 1 ga Satumbar 2026.
“Na ga kun yi kokari sosai a wasan sada zumunta da kuka buga da kasar da ta dauki bakuncin ku, kun jajirce har kuka samu nasara. NFF da daukacin ‘yan Najeriya suna alfahari da ku,” in ji shi.
“Nasara da kuka samu a kan Poland ta kara karfafa muku son sake yin nasara, kuma idan kuka sake samun nasara a kan ƙasar Koriya a ranar Talata, zai kara karfafa muku ruhin ku, inda zaku kara samun kwarin gwiwa da kuzari na fuskantar kalubalen wasannin matakin rukuni na Kofin Duniya. Ina kira gare ku ku fita neman nasara ba tare da jinkiri ba a kan ‘yan Korea.”
Najeriya za ta buga wasan Rukuni na F na Gasar Duniya tare da Spaniya, da China, da kuma New Caledonia.
Falconets za ta fara da Spaniya a ranar Litinin, 7 ga Satumba, sannan ta buga da China a ranar 10 ga Satumba, kafin su kara da New Caledonia a ranar 13 ga Satumba.